Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Yankin Tafkin Chadi Zai Taimakwa Mutanen Yankin

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mummunan ayyukan da masu tayar da kayar baya da suka tafka a yankin tafkin Chadi tun daga shekarar 2009 ya sanya miliyoyin mutane sun rasa gidajensu tare da lalata kadarorin da suka kai na biliyoyin nairori wanda ya shafi rayuwar wadanda suka tsira daga hare-haren.

A kokarin ta na tabbatar da bukatun wadanda hare-haren ta’addancin ya rutsa da su da nufin taimaka musu, Hukumar Tafkin Tafkin Chadi (Lake Chad Basin) ta bukaci kasashen yankin da su tsara wani shiri na Aiki kan ginshikai tara na dabarun wanzar da zaman lafiya a yankin.

Ginshikan su ne Hadin gwiwar siyasa, Taimakon Jama’a, Tsaro da ‘Yancin Dan Adam, kwance damara, Ragewa, Gyarawa da sake hadewar mutanen da ke da alaka da Boko Haram.

Sauran su ne Taimakon Jin kai, Shugabanci da kwangilar zamantakewar, farfado da zamantakewar tattalin arziki da Dorewar Muhalli, Ilimi, Gina zaman lafiya, Karfafawa da hada mata da Matasa da sauransu .

Da yake jawabi a taron da aka gudanar a Jami’ar Amurka ta Najeriya dake Yola Kwamishinan Jiha na sake ginawa, da ayyukan dan Adam Mista Elijah Tumba ya bayyana cewa Sake Binciken Fasaha a Jihar ta Adamawa Tzai taimaka a bangarori da dama na bunkasa rayuwar bil adama da samar da zaman lafiya a jihar Adamawa.

Leave a Reply