Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Yan Wasan Super Eagles Zasu Fara Shirye Shiryen Buga Wasa Kwallon Kafa Na Afrika

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yan wasan Super Eagles zasu fara shirye shiryen buga wasa kwallon kafa na Afrika tare da jamhuriyar Benin da Lesotho.

Yan wasan sun ziyarci wajen dakin motsa jiki na otal din Eko domin shirin wasan na ranar Talata a filin wasan Teslim Balogun.

Paul Onuachu and Alex Iwobi daga Everton suna cikin wadanda zasuyi wasan.

Zuwan Paul ya bada mamaki ga yan Belgian yayin da suka hana yan wasan su fita kasashe sakamakon bullar cutar corona.

Ahmed Musa, Ola Aina, William Ekong, Henry Onyekuru, Semi Ajayi, Oghenekaro Etebo da Shehu Abdullahi sune yan wasan farko da suka isa sansanin samun horo.

Ana sa ran adadin yan wasan zai karu kafin a fara horon farko.

Sannan tawagar yan wasan zasu tashi zuwa jamhuriyar Benin a ranar Alhamis tare da mai bada horo Gernot Rohr.

Leave a Reply