
Yan wasan kwallon kafa yan kasa da shekara 17 na kasar Kamaru su lallasa takwarorinsu na kasar Guinea da ci 3-2 a wasan kasashen Africa wato AFCON wanda aka gudanar a kasar Tanzania.
An gudanar da wasan ranar Lahadi a filin wasa na Dar es Salaam, inda fanaliti ta biyo baya.
Yan wasan Guinea sun lallasa Najeriya da fanariti 10-9 a wasan kusa da karshe, sai kamaru da ta lallasa Angola.

Wan nan ne karo na biyu da kasar ta Kamaru ta lashe kofin a wasan AFCON na yan kasa da 17.
