Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane 2 Masu Satar Kayan Wutar Lantarki.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Yagana Ali, Adamawa
Wasu jami’an tsaro masu aikin sintiri a kan hanyar Rugange zuwa Njoboliyo sun kama wasu mutane biyu masu satar kayan jama’a.

Wadanda ake zargin Idi Wakil mai shekaru 62 da Babangida Bello mai shekaru 54 mazauna Madumari dake karamar hukumar Yola ta kudu an kamasu suna sanar igiyar wutar lantarki da ya hada Njoboliyo sa sauran kauyuka daga Yola, wanda ya jawo rashin wutar lantarki a yankin kuma yake jawo matsala ga kamfanin rarraba wutar lantarki.

Wannan ya fito ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda Suleiman Yahaya Nguroje ya fitar.
Yace kwamishinan yan sandan jihar Aliyu Adamu Alhaji ya yabawa jami’an sa da ma’aikatan wutar lantarki wajen tabbatar da kama masu laifin.

Bincike ya nuna cewa masu laifin sun taba aiki da kamfanin rarraba wutar lantarki kuma sun sha aikata irin wannan laifin tun shekarar 2018.

Daga karshe kwamishinan ya umurci jami’an sa da cewa da zarar sun kamala bincike su tura masu laifin zuwa kotu, kuma ya bukaci hukumar kamfanin rarraba wutar lantarki da su amshi igiyar wutar a shalkwatan yan sanda na jihar.

Leave a Reply