‘Yan Najeriya 10 Sun Gudu Daga Gidan Yarin India

‘yan Najeriya guda 10 da ba’a tantance ko su waye ba sun gudu daga gidan yari da ake tsare dasu a kasar India.

Ata bakin Business Standard sun bayyana cewa ‘yan Najeriyar da ‘yansandan Gautam Buddh Nagar suka tsare sun karya inda ake tsare dasu sun gudu inda aka sake kama wasu daga cikinsu.

Haka nan Darakta Janaral na ‘yansandan Meerut sunce ‘yan fursunan sun gudu sakamakon rashin tsaro na musamman da akayi musu amma an kama wasu kuma an dauki mataki kan ma’aikatan ta suke da hannu.

‘yansandan Uttar Pradesh sun kama kimanin ‘yan kasashen waje 60 da basu da takardun zama ko ake zarkin suna aikata laifuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *