‘Yan Majalisar Wakilan Najeriya Sun Gayyaci Buhari

Yan majalisar tarayya sun gayyaci shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, don ya bayyana matakan da ya dauka kan sha’anin tsaro a kasar.

Wan nan ya biyo bayan bayanin da dan majalisar jihar katsina yayi a majalisa, Dayyabu Safana yace kullum ana kashe mutane ba adadi ana lalata dukiyoyin al’umma a tsakanin Safana/Batsari/Dansamu a jihar Katsina.

Dayyabu-Safana yace a yankin da yake wakilta na fama da hare-haren yan bindiga wanda ya kamata shugaban kasar yasa dokar ta baci a yankin.

Hare-haren a yankin ya kai matuka inda maharan naci gaba da kisan mutane ba ji ba gani kuma su kona gidajensu. Ya kara da cewa cikin awa 48 an kaiwa fiye da kauyuka hudu da yake wakilta hari.

Majalisar ta kirayi gwamnatin tarayya data tura jami’an soji don su taimakawa jami’an yansanda da ragowar jami’an tsaron da ke yankin a samu a kakkabe yan bindigar.

Haka nan sunyi kira da a kafa hukumar bada agajin gaggawa ta kasa a yankin don su dinga bada taimakon gaggawa ga wadanda rikicin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *