Yan Majalisar Najeriya Sun Marawa Dokar Kaddamar Da Ranar June 12 A matsayin Ranar Demokaradiyya

house-of-senate
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin kasar najeriya ta sanya hannu a wani kudiri domin a sanya ranar 12 ga watan yuni na kowace shekara a matsayin ranar demokradiya.

An shigar da kudirin ne a zauren majalisar dattawa bayan shugaban masu rinjayi a majalisar wato Ahmed Lawan ya gabatar da rahoton ga yan majalisan a ranar alhamis da ta gabata.

Haka nan a watan December da ta gabata yan majalisun wakilai sun gabatar da kudirin inda suka kara maimaita shi ranar alhamis.

Yan majalisun sun nemi chanza kudirin ya zama doka bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyanar da kudirin.

A watan yuni data gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za’a ringa gudanar da ranar demokradiya a kowace rana ta sha biyu ga watan yuni.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wannan kudirin bayyan an karrama mari gayi Moshood Abiola wanda ake kyautata zaton shiya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 1993.

Related stories

Leave a Reply