Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Yan Kungiyar ISWAP Sun Kai Hari Damasak Na Jihar Borno

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wasu masu tayar da kayar baya na kungiyar Islamic State West Africa (ISWAP), sun kai wani mummunan hari tsakanin yammacin Lahadi da safiyar Litinin, a yankin Damasak na jihar Borno, dake Arewa maso gabashin Najeriya.

Damasak na kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Nijar, wanda keda nisan kimanin kilomita 180 a Arewa maso Yammacin Maiduguri.

Dandal Kura Radio International ta fahimci cewa wasu masu aikin jin kai sun tsere ta kogin Komadougou dake jihar Yobe, yayin da sojoji suka shiga aikin fatattakar maharan.

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta aika da jiragen yaki domin tallafawa sojojin kasa don tunkarar kutsen da suka hada da manyan motocin daukar bindiga 20, ranar Lahadi.

Gidan Rediyon Dandal Kura ya kuma gano cewa maharan sun dawo da safiyar Litinin kuma sun ɗan shiga cikin garin Damasak kafin sojoji su fatattake su.

An ruwaito cewa sojoji biyu da maharan ISWAP 39 ne suka rasu a ranar Lahadi yayin da sojojin Najeriya da na Nijar suka fafata da maharan.

Harin na yanzu yana daga cikin jerin matsalolin tsaro da ake kaiwa garuruwan wanda ke kawo matsala ga jami’an tsaro, da kuma kawo cikas ga ayyukan agaji a Arewa maso gabashin Najeriya.

Nganzai, Ngala, Kaga, Marte, Monguno, Dikwa na daga cikin wuraren da dakaru suka yi arangama da mayakan na ISWAP a kwanakin nan.

Abadam, Kukawa, Guzamala da Marte kuma sune wurare masu haɗari a halin yanzu.

Leave a Reply