Yan Boko Haram Sun Nuna Bidiyon Jirgin Sojan Sama Najeriya Daya Bata

Rundunar Sojin saman Najeriya ta rasa hanyar sadarwa da jirgin ta na Alpha Jet da ke gudanar da aikin yau da kullun a yammacin Laraba a yankin dajin Sambisa dake Arewa maso gabashin Najeriya.

An nuna wani abu mai fashewa ya lullube jirgin saman sojin saman Najeriya na Alpha Jet daga bidiyon farfaganda da aka saki 2 ga Afrilu, 2021.

Hoton bidiyo daga farfaganda da aka fitar ranar 2 ga watan Afrilu na shekarar na da tsawon mintuna bakwai da dakika 30 inda ya nuna jirgin Alpha Jet yana ta shawagi kasa-kasa a filin tare da mayakan Boko Haram da yawa inda suke bashi wuta.

A bidiyon ana iya ganin maharan suna harbi da manyan bindigogi harbor jirgin sama.

Sannan ana iya ganin hotunan fashewar wani abu mai wuta, yayin da jirgin saman na Alpha Jet ya doshi zuwa ƙasa cikin sauri.

Daga baya mayaka sun koma yankin da hatsarin ya faru kuma suka fara kwashe kayan jirgin da kayayyakin matukan jirgin.

Bidiyon ya kuma nuna wasu mayaka wanda suka rufe fuskokinsa dauke da bindiga a tsaye a kan jirgin, kuma yana magana da larabci da Turanci.

An kuma nuwa wasu mayakan na Boko Haram da yawa dauke da motocin daukar bindiga, babura, bindigogin AK samfurin, injunan sanya bel da kuma wasu manyan bindigogi na hannusu da kuma Motar dauke da Bama-bamai .

Wannan lamarin ya haifar da damuwar kan sha’anin tsaro da jiragen sama na soja harma da na agaji da ke shawagi a yankin da ake fama da rikicin duk dab a tabbacin su suka harbor jirgin.

Jirgin na Alpha Jet kwararren jirgi ne da ake horaswa dashi da kuma kai hare-hare wanda yayi aiki na kusan shekaru 30, tare da Sojojin Sama wanda aka kawo daga Amurka.

Tun da farko, Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet na rundunar , ya bayyana sunayen matukan kamar haka Laftanar John Abolarinwa da Laftanar Ebiakpo Chapele.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *