Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

WHO Tayi Bikin Tunawa Da Ranar Tarin Fuka Na Duniya

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil, Maiduguri
Hukumar lafiya ta duniya ta (WHO) tayi bikin tunawa da ranar tarin fuka na duniya wanda ake gudanarwa a ranar ko wane 24 ga watan Maris na kowace shekara domin wayar da kan jama’a game da mummunan cutar, da kuma kiwon lafiya, da zamantakewar jama’a da tattalin arziki, da kuma kara kaimi wajen kawo karshen cutar a duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana hakan ne a shafin yanar gizon yau don bikin ranar tareta duniya.

Har ila yau, an bayya cewa ranar an fara gudanar da ita a shekarar 1882 lokacin da Dr Robert Koch ya sanar cewa ya gano kwayar cutar da ke haifar da tarin fuka, wanda ya bude hanyar ganowa da warkar da wannan cuta.

WHO ta ci gaba da cewa, tarin fuka ya kasance daya daga cikin cutuka masu saurin kisa a duniya, inda a kowace rana, kusan mutane 4000 na rasa rayukansu da mutane 28,000 dake kamuwa da cutar. suna rashin lafiya tare da wannan cuta mai wahalar magani.

A Kokarin da hukumar lafiya take yi na yaki da cutar ta hukumar ta ceci kimanin rayukan mutane miliyan 63 tun daga shekarar 2000.

Kwamitin kula da lafiya na duniya ya tuhumi shugabannin duniya da su kara himma da jajircewa don kawo karshen cutar tarin fuka a duniya baki daya.

Haka nan hukumar tace annobar cutar 19 da ta kawo cikas wajen cigaba da karshen cutar ta tarin fuka da tabbatar da kariya daga cutar.

Leave a Reply