Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Wasu Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Sunyi Hadin Gwiwa Da Gwamnatin Jihar Borno kan Samar Da Ruwa

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyoyi masu zaman kansu na Action Against Hunger da WASH da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Borno zasu samar da tsaftataccen ruwa musamman ga mutanen da ke rayuwa cikin tashin hankali da wuyarshiga.

Manajan Action Against Hunger Kolo Dunoma da takwaransa na a jihar Borno, Mista Dare Oduluyi ne suka bayyana hakan yayin bikin ranar Ruwa ta Duniya ta 2021 a ranar Litinin tare da Jigo.

Taken ruwan na shekarar nan shine ‘Darajar Ruwa’ wanda aka gudanar a Cibiyar Forsham da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

Dunoma ya ce, shirin yaki da yunwa sun kaiwa sama da mutane miliyan 2.5 masu bukatar abinci a arewa maso gabas tare da sake ginawa da kuma gyara rijiyoyin burtsatse da ake da su, inda mutane 771,593 a jihohin Borno da Yobe suka amfana.

Hakanan sun gina wasu 17 a kananan hukumomi hudu na Kaga, Nganzai, Monguno da Damboa.

Hakazalika, a cikin shekarar 2019, ya ce, kungiyar AAH ce ta gudanar da bincike a Borno kuma ta zo da wasu Matakan Aiki, wadanda suka hada da kafa kungiyar teburin ruwa na jihar ta Borno wanda Mataimakin Gwamnan, Umar Usman Kadafur ya jagoranta a shekarar 2013.

A nashi jawabin, Kwararren Masanin na WASH, Mista Oduluyi ya ce, “ba tare da samun ruwa mai tsafta cikin sauki ba, rayuwar mutane zata kasance cikin rashin lafiya, talauci da kuma wahalar tara ruwan.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, wanda Mataimakin Daraktan Gudanarwar a ma’aikatar, Mista Saleh Adamu Bata ya wakilta ya gode wa Action against hunger da sauran wadanda wadanda akayi hadin don samar da tsaftataccen ruwa mai tsafta ga al’ummarta da zai ceci rayuwar mutane.

Leave a Reply