
Wani mazaunin Unguwar Gwazaye da ke karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, Awaisu Nagyala, ya yi wa ɗansa mai shekara 18 dukan tsiya. , Abba Awaisu, wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa.
An bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da Nagyala ya zargi dansa da satar galan biyu na manja.
Wani shaidar gani da ido, Kabiru Usman, wanda ya ce Nagyala tun da farko ya kulle gida ya kuma yi wa dan nasa mummunan rauni da sanda, ya kuma bayyana cewa wasu makwabta, wadanda suka yi yunkurin ceton yaron, mahaifin ya gargade su dakarsu shiga harkar sa.

A nasa martanin, Shugaban Unguwar Gwazaye, Bello Rabi’u, ya ce yaron da aka kasha din anyi hanzarin kai shi asibitin dake kusa cikin mawuyacin hali, inda aka tabbatar da cewa ya mutu.
Lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Abdullahi Haruna, ya ce har yanzu bai samu labara kan lamarin ba, amma ya yi alkawarin sanar da manema labarai da zaran ya samu cikakken bayani.
