Wani Mutum Na Kasa Kaya A Bakin Titi Bayan Aikin Shekaru 35 A Matsarin Malami A Jihar Borno

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wani dattijo mai suna Al-Amin Shettima Bello, a jihar Borno wanda ya gudanar da aikin gwamnati a matsayin malami shekaru 35 na nan a tituna a birnin Maiduguri yana talla.

Shettima Bello ya bayyana wa manema labarai cewa turawa ne suka koya masa.

Yace a zamanin da yake makaranta, Malamai bakaken fata kadan ne kamar su marigayi Dr. Shettima Ali Monguno, Shettima Kashim da marigayi Shettima Mustapha Kutai (mahaifin sanata Kashim Shettima).

Malam Bello ya bayyana wa manema labarai a bakin hanya cewa Farfesa Bosoms Sheriff na jami’ar Maiduguri dan makarantar su.

Bello wanda yake zama a kusa da bankin First Bank ATM dake kusa da kasuwar Monday Market a birnin Maiduguri yace yana zama a wan nan gurin nan saboda masu zuwa daukan kudi na iya sayan kayansa cikin sauki da zarar sun dauki kudinsu.

Ya kuma ce ya zabi said a Rub ne saboda don samun samun bun kashewa da kuma yadda mutane ke bukatar sa a wan nan lokacin.

Shettima Bello yace yasan akwai wadanda sukayi karatu tare da suka samu rufin asiri amma wasu sun manta dashi ko kuma inda yake.

Leave a Reply