Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Wani Bakon Cuta Ya Kashe Wasu Mutane 3 Tare Da Kwantar Da Mutane Dari 2 Da 84 A Jihar Kano.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu mutane 3 sannan 183 suna kwance a gadon asibiti wanda ake zargin sun sha wani lemon da lokacin amfanin shi ya kare.

Kwamishinan lafiya ta jihar Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa yace hakan ya shafi kanana hukumomi 13 a jihar.

Kwamishinan ya shaidawa manema labarai a Kano cewa lamarin ya faru bayan wadan da abin ya shafa sun sha lemon samfurin Jolly.

Yace wa’adin amfanin sa ya kare tun kusan shekara guda amma haryan zu ana saidawa a kasuwa.

Yace mutane dari 2 da 84 ne abin ya shafa, an salami 101 a yanzu kuma 183 ne suke kwance a asibiti inda suke samun kulawa.

A yanzu dai kwamishinan lafiya yace ma’aikatar sa sun kwato kayakin da lokacin amfanin su yak are wanda ya kai kimanin naira miliyan 59.

Dr. Bashir Lawan likita a ma’aikatar lafiya yace alamun cutar suna kama da alamun dake tarwatsa hanyoyin jinni na dan adam.

Leave a Reply