Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

UNICEF Zata Tantance Yara Kanana Miliyan 3 Kake Fama Da Cutar Tamuwa A Yankin Arewa Maso Gabas

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Asusun tallafawa yara kanana na majalisar dinkin duniya UNICEF ta ware kudade domin tantance yara akalla miliyan uku dake fama da tsananin tamuwa a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Shugabar sadarwar hukumar a Najeriya, Folashade Adebayo ne ta bayyana hakan cikin sanarwa data fitar litinin a birnin Maiduguri.

Tace za’a gudanar da tantacewar ne da kudade da gwamnatin kasar japan ta bayar, kuma zai taimakawa UNICEF matuka wajen aiki da uwaye da sauran masu kula da ya’ya wajen bunkasa abinci a yankuna.

Sanarwar na kunshe da cewa, hukumar zata saka ido wanda tsamo yara masu fama da tsananin tamuwar a jihohin Borno da Yobe wanda kiyasi da akayi kwanan nan ya nuna cutar tamuwar ya karu da kashi 10 a Borno, kashi 12.3 a kuma a Yobe cikin watanni wanda tace annobar COVID-19 da rasa ayyuka yi, dama rashin tsaron abinci, ka iya jefa daruruwan yara a yankin cikin hatsarin kamuwa da cutar Tamuwa a karshen shakrar nan.

Adebayo ta kuma ce, za’a bada horaswar yadda za’a adana da girka abinci masu sauki ga mata masu juna biyu, sai masu shayarwa da sauran masu bada kula su dubu hamsin, a game da yadda zasu kula da ciyarwar ya’ayan su da kuma gane matakin lafiyar su.

Leave a Reply