UNDP Ta Kaddamar Da Gagarumin Shiri Wajen Farfado Da Tattalin Arzikin Yankin Tafkin Chadi

undp2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya ta kaddamar da gagarumin shiri wajen farfado da tattalin arzikin yankin tafkin Chadi.

Wan nan shirin, zai lankwame miliyoyin daloli wanda kasashe guda hudu dake yankin tafkin chadi sukayi maraba da shi. Wan nan shirin sabon tsari ne na hadin gwiwa domin ceto yankin.

Shirin zaifara aiki daga 1 ga watan Satumba 2019 kuma zai dauki tsawon shekaru biyu. Shirin zai mamaye kasashe hudu na yankin Tafkin Chadi, kasahen sune Kamaru, Chadi, Nijar da Najeriya.

Kuma yana da burin aiwatar da shiri na gaggawa domin taimakawa hukumomin al’umma domin dakile ayyukan kungiyar Boko Haram. Haka nan, wan nan zai bada damar samar da jami’an tsaro na farin kaya da kuma samar da abubuwan more rayuwa da mutane suke bukata da ayyukan dogaro da kai.

Wan nan shiri da aka gabatar na daya daga cikin muhimman batutuwa da aka gabatar a wajen taron kungiyar gwamnonin yanki Tafkin Chadi karo na biyu wanda aka bude a yau a birnin Niamey dake jamhuriyar Nijar. Wan nan shirin yana karkashin hukumar dake lura da yankin Tafkin Chadi da agazawar kungiyar tarayyar Afirika. Jamhuriyar kasar Nijar ce ta zama mai masaukin baki inda gwamnatin kasar Jamus ta samar da kudaden gudanar da wan nan taron.

Yayin da yake Magana wajen bude taron karo na biyu na gwamnonin dake yankin Tafkin Chadi, Daraktan Dake kula da yankin Afrika ta hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya, Madam Ahunna Eziakonwa tace wan nan shirin na farfado da yankin Tafkin Chadi, zai bada damar da mutane zasu sake sabuwar rayuwa musamman mata da matasa wanda sune rikicin ta’addancin yafi shafa.

Ta kara da cewa, idan aka saurari koke-koken al’umma, wanda ya hada da kaura da mutane sukayi daga muhallansu, zai sa a samu dawamamman tsaro da kuma farfado da yankin Tafkin Chadi.

A jawabin ta, Madam Corinna Fricke, babbar jami’a daga ofishin harkokin kasashen waje na kasar Jamus, tace wan nan sabon tsarin da zai samar da kudade daga kasa da kasa domin farfado da yankin, zai tabbatar da inganta rayuwar mazauna yankin tare da cike duk wani gibi da shirin yake dashi a yanzu.

Wan nan shirin na farfado da yankin Tafkin Chadi, wanda shine irinsa na farko, ya samu amincewar hukumar dake kula da yankin Tafkin Chadi wanda kuma ‘yan hukumar suka amince dashi a watan Agustan shekarar 2018, kuma ya samu amincewar majalisar tarayyarar kasashen Afrika mai kula da zaman lafiya da samar da tsaro a watan Disamban skekarar 2018.

Related stories

Leave a Reply