Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Tsaro Lamari Ne Da Ya Shafi Kowa Da Kowa Inji Sanda Sheriff

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban Kwamitin Hulda da Jama’a na ‘Yan Sanda (PCRC) reshen jihar Borno Eng Sanda Sheriff ya ce tsaro lamari ne da ya shafi kowa da kowa kuma bai kamata ace ma’aikata cikin kaki ne kawai zasu su aiwatar da shi ba.

Sanda Sheriff ya bayyana hakan ne yau a taron PCRC da aka gudanar a ofishin ‘yan sanda hedikwatar su dake Maiduguri a yau.

Wakiliyar mu Aish Mustapha Kolomi ta ruwaito cewa taron na shekara-shekara na tsaro ya samu halartar wakilai da dama daga dukkan kananan hukumomin 27 na jihar.

Injiniya Sanda Sheriff ya ci gaba da cewa batun rashin tsaro ba hakkin jami’an tsaro ba ne kawai don magance shi amma yana bukatar hadun kai tsakanin al’umma da kungiyar tsaro.

Ya kara da cewa tayar da kayar baya da sauran nau’ikan laifuka na ci gaba da karuwa a kullum.

Ya shawarci membobin jama’a da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro don samun ci gaba mai dorewa a jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa tare da hadin kai, da aiki tare dukkan nau’ikan laifuka za a rage su zuwa inda za’a hada karfi da karfe don kawo karshen wannan rashin tsaro.

Jagoran kungiyar da ke hulda da’ yan sanda ya ce halin da ake ciki a jihar Borno akwai matukar damuwa wanda ake dashi fiye da shekaru 10 a yanzu, duka gwamnatin tarayya da ta jihar suke kashe makudan kudade don ganin sun kawo karshen rashin tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar.

Haka nan Ya yi kira ga ‘yan kasar da su hada karfi da karfe da jami’an tsaro don kawo karshen ta’addancin, a jihar Borno da ma kasa baki daya.

Leave a Reply