Sufetan Yan Sanda Kasa Ya Bada Umarnin Bada Cikakken Tsaro A Duk Fadin kasa

POLICE-IG-ADAMU
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sufeta janar na yan sanda Mohammed Adamu, yaba da umarnin bada cikakkiyar tsaro dama aikin patrol a dukkan jihohin najeriya da Abuja cikin gudanar da bikin kirsimeti da kuma sabon shekara.

Sufeta Adamu ya bada umarnin ne ga dukkan mataimakan sa da kwamishinonin yan sanda a jihohi na cewa su tabbatar an gudanar da bikin cikin zaman lafiya.

Frank Mba jami’i mai hulda da jama’a na kwamishinan rundunar yan sandar ne ya fitar da hakan cikin sanarwa.

Haka zalika sufetan yan sandan ya bada umarni ga rundunar da suyi amfani da sirri da sauran kayakkain aikin su a manyan hanyoyi, filin jiragen sama dana kasa, wajajen ibadu, wajajen shakatawa da sauran su don bada tsaro.

Yace yan sandan bazasu lamunci duk wani abu da zai takurawa matafiya ba sannan ya godewa dukkan yan najeriya bisa goyon baya da suke baiwa rundunar yan sandar kasar cikin yakan ayyukan bata gari da sukeyi.

Leave a Reply