Sufeta Janar Na Yan Sanda Ya Amince Da Nadin Sabon Kwamishinan Yan Sanda.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sufeto Janar na yan sanda Usman Baba Ali ya amince da nadin Abdu Umar a matsayin sabon kwamishinan yan sandan jihar Borno.

Sabon kwamishinan yan sandan ya kama aiki jiya a shalkwatar rundunar yan sandan jihar Borno kuma ya gudanar da muhimman ayyuka da yawa don taka muhimmiyar rawa don kare rayuka da dukiyoyin yan kasa a jihar.

Kwamishinan ya ce ba shi da wani zabi bayan nadin da sufeta janar ya yi masa zuwa jihar Borno don sauke nauyi da kundin tsarin mulkin kasa ya ba shi na yi wa mutanen Borno hidima tare da jami’an jihar da goyon bayan kafafen yada labarai.

Abdu Umar ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishinsa.

Sabon kwamishina yan sanda ya sake nanata cewa yana sane da duk abin da ke faruwa a arewa maso gabas, ya cewa yana nan don hidima ga kowa da kowa daidai gwargwado, ya tabbatar da cewa ƙofofinsa a bude suke don bada labarai da mu’amala da jama’a tare da cimma ayyukan yan sanda haka kuma yan jaridu zasu iya taka muhimmiyar rawa.

Yan sanda a karkashin jagorancinsa za su yi aiki tukuru don kawar da ire -iren laifuka ta hanyar kamawa da gurfanar da masu laifin tare da aiwatar da dokoki da umarni tare da alwashin yin aiki bisa hangen nesa.

Daga karshe yayi alkawarin yin aiki tare da dukkan hukumomin tsaro a jihar musamman a wannan lokacin da yan ta’addan Boko Haram ke mika wuya kusan kullum

Leave a Reply