Sudan Ta Rufe Iyakokin Kasa Dake Tsakinta Da Makotanta

Ma’aikatar tsaron kasar Sudan ta bayyana cewa ta kulle iyakokin shiga kasar ta kasa da kasashen dake makotaka da ita ciki harda kasar Chadi.

Wadan da abun ya shafa harda kudancin Sudan, Misra, Libya, Afrika ta tsakiya, Ethiopia and Eritrea.

Sun yanke wan nan hukuncin ne saboda daukar matakan gaggawa bayan saukar sugaban kasar Hassan Omar al-Bashir. Chad da Sudan na da nisan kilomita 1360 a tsakaninsu.

Sudan na hada-hadar kasuwanci inda yan kasuwa da dama suke cinikayya tsakanin Sudan zuwa gabashin Chadi.

Shugabannin Chadin na nan na kokarin ganin sun kawo karshen shigo da abubuwan da basu dace ba musamman sukari daga Sudan don su ceci kamfanin Sukari na kasar Chadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *