Jami’an Tsaron Najeriya Sun Yiwa Boko Haram Kwantan Bauna A Damaturu

Bayan da aka samu sahihan bayanai kan shirin da mayakan Boko Haram suka yi na kai hari garin Damaturu, dake jihar Yobe a Arewa maso gabashin Najeriya, sojojin Najeriya dake shiyya ta 2 karkashin Operation Lafiya Dole, sun samu nasarar yiwa yan ta’addan kwantan bauna inda suka kashe yan kungiyar Boko Haram da dama yayin da sukayi niyyar kai harin cikin garin Damaturu a jihar Yobe ranar Talata da karfe 5:15 na yamma.

Yan kungiyar sa kai sun samu nasarar yiwa yan ta’addan kwantan bauna a garin Maisandari dake wajen birnin Damaturu.

Jami’an sojin sun samu nasarar dakile harin tare da taimakon jami’an sojojin sama. Haka nan da yawa daga cikin yan ta’addan sun gamu da ajalinsu inda wasu suka samu raunuka, haka zalika an samu makamai da dama.

Jami’an dai naci gaba da neman wadan da suka tsere don su samu su kakkabe yankin gaba daya.