Sojojin Najeriya Sun Maida Mutanen Jakana Birnin Maiduguri

Sojojin Najeriya sun kwashe mutanen garin Jakana dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya zuwa sansanin yan gudun hijira na Bakassi dake birnin Maiduguri sakamakon hare-haren Boko Haram a yankin.

Jakana, na da nisan kilomita 40 zuwa Maiduguri a kan titin Maiduguri zuwa Damaturu. A farkon shekarar nan ne yan ta’addan suka kai hari garin har da gurin yansanda dake yankin.

Manema labarai sun samu rahoton cewa an fara kashe mutane tun ranar litinin da yamma, inda wakilin mu ya tabbatar mana cewa yayin da ya isa sansanin yan gudun hijirar na Bakassi ranar Talata ya tarar da manyan motoci kimanin su 30 suna sauke mutanen Jakana.

Wani mazaunin yankin Alhaji Adamu Hassan ya bayyana cewa ranar litinin da safe shugabannin yankin sun kira yan garin cewa su rantse da Alkur’ani mai girma kan basa taimaka wa ‘yan ta’adda ta kowace hanya.

An nemi jin ta bakin sojoji, yansanda da jami’an NSCD da suka yi rakiyar mutanen amma basu tofa komai ba. Mai Magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa ta kasa a Arewa maso gabas Abdulkadir Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *