Sojojin Najeriya Sun Kwace Kifi Da Fatu Daga Kungiyar Boko Haram

nigerian-army-training-702x336-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A yunkurinsu na dakile hanyoyin samun kudin shiga ga mayakan Boko Haram, rundunar sojin Operation Lafiya Dole sun lalata motoci hudu shake da bandan kifi da kuma fatu wadanda aka saje da buhunan wake a hanyar Gamboru- Ngala.

Ya yin lalata kayayyakin kwamandan shirin Operation Lafiya Dole Manjo Janar Olusegun Adeniyi, ya bayyana cewa mayakan Boko Haram suna amfani da kasuwancin kifi domin samun kudin shiga na gudanar da aikace-aikacen su.

Janar Adeniyi, ya kuma kara da cewa an cafke morocin ne shake da kifayen wadanda za a je a yi cinikinsu domin baiwa mayakan Boko Haram domin cigaba da ta’addanci.

Hakazalika ya ce wadanda ake zargin za a gurfanar da su gaban kotu domin cigaba domin kamala bincike. Ana zargin mayakan na Boko Haram suna kwace kudade daga hannun jama’a domin gudanar da ayyukansu na ta’addanci a yankin tabkin Chadi.

Related stories

Leave a Reply