Sojojin Najeriya Na Cigaba Da Farautar Yan Boko Haram

nigerian-army-training-702x336-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojin najeriya sun bayyana cewa jami’ansu naci gaba da farautar yan kungiyar Boko Haram a jihar da ragowar bangarori a arewa mmaso gabas.

Mai kula da ayyukan rundunar ta fannin yada labarai Col. Aminu Iliyasu ne ya bayyana hakan a Abuja.

Iliyasu yace jami’an sashin na 3 karkashin Operation Lafiya Dole ya samu karin makamai na AK47 guda 4, bindigar RPG ) da kuma mota mai dauke da harsashi. 

Ya kara da cewa jami’an sun samu wata mota mai bindiga akai  da suka yar, babur guda 1 wanda duk mallakar yan Boko Haram din da suka gusu ne.

Haka nan jami’ansu dake Gubio sun samu nasasar dakile wani harn nan Boko Haram attack a matsuguninsu inda suka kashe mutum daya suka samu bindigar AK47 guda 1, magazine 1, Radio 1, wayar sadarwa 1 da kuma sirinji da allurai.

San nan jami’an dake bataliya ta 231 Battalion sun kama wani dan kungiyar ta Boko Haram mai suna Baana Zakari wanda aka fi sani da Okocha a tashar Biu, wanda shine yake kai musu bayanan sirri. Haka nan sun kama wani mai suna, Alhaji Lawan, wanda aka fi sani da Caffenol a gurin bincike dake Maina Hari wanda yake kai musu kayyayaki.

Iliyasu ya kara da cewa jami’an sun kama wani dan kungiyar ISWAP Usman Yage, dan kasar Chadi wanda yake da alaka da manyan kwamandojin Boko Haram da ISWAP.

Related stories

Leave a Reply