Sojojin Najeriya Da Kamaru Sun Kashe Boko Haram 27 A Jihar Borno

Rundunar sojojin Najeriya shiyya ta daya a bangaren OPERATION LAFIA DOLE da hadin gwiwar jami’an sojin Kamaru sunyi arangama da yan kungiyar Boko Haram a kauyukan Wulgo, Tumbuma, Chikun Gudu da Bukar Maryam dake kusa da tafkin chadi a arewacin jihar Borno dake arewa maso gabshin Najeriya.

Rahoton ya fito daga jami’in rundunar mai hulda da jama’a na rundunar Colonel Sagir Musa, inda yace jami’an sun kashe yan ta’adda 27, yayin da suka gudanar da aikin.

Ya kara da cewa sun samu muggan makamai da dama daga gun yan ta’addan, motoci, injin nika da kuma tutarsu, haka nan ya tabbatar da cewa ba’a samu asarar rai ta bangarensu ba.

Haka nan ana gudanar da wani aikin a yankin Gombaru – Ngala da kewaye don kakkabe yan ta’addan daga yankin wadanda suke tserewa daga jami’an hadin gwiwa na OPERATION YANCIN TAFKI yayin da suka je maboyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *