Sojoji Sunyi Nasarar Hana Harin Da Yan Ta’adda Suka Kai

DHQ TROOPS
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sojoji karkashin shirin Operation Whirl Stroke sunyi nassarrar hana harin da yan ta’adda suka yi niyar kaiwa matafiya tare da kashe wasu daga cikinsu a jihohin Plateau, Benue da Taraba.

Shugaban sashin yada labarai na sojin kasar manjo janar John Enenche shine ya bayyana hakkan kuma yace sojojin sunyi nassarar kwato makamai da dama da kuma Babura.

Yace sojojin sunyi nasara ne sakamakon kaimi da suka kara wajen ganin yakin arewa maso tsakiya ya kubuta daga hannun yan ta’ada tare da ganin anyi bikin karshen shekarrar cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply