
A cigaba da kokarin kakkabe yan kungiyar ISWAP da rundunar sojin saman Najeriya suke yi a yankin tafkin Chadi sun samu nasarar latata gurare da kayayyakin yan ta’addan a kauyen Tumbun Kaiyowa dake arewacin Borno.
Rahoton ya fito daga mai Magana da yawun rundunar sojin saman air Kwamanda Daremola.
Ya bayyana cewa bayan samun bayanan sirri daga jami’ansu sun samu nasarar lalata kaya da guraren yan ta’addan a wani daji mai tarin bishiyoyi.
Jirginsu na Alpha Jet ne ya samu nasarar lalata guraren inda bayan ya dake su suka kama da wuta.
An samu an kashe da yawa daga cikin mayakan ISWAP yayin harin, haka nan sun hada kai da jami’an sojin kasan don karasar da ragowar a Arewa maso gabas.
