Shugabannin Kasashen ECOWAS Sunyi Alla Wadai Da Yunkurin Juyin Mulki A Ethiopia

Ethiopia
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasashen ECOWAS a madadin shugabanin kasashen Muhammadu Buhari yayi alla wadai da yunkurin da aka kai na kifar da gwamnatin kasar Ethiopia ranar 22 ga watan Yuni na shekarar 2019.

Ya bayyana hakan ne cike da tausayi da gaisuwa ga iyalan wadanda yunkurin ya ritsa dasu da kuma gwamnatin kasar ta Ethiopia.

San nan ya jaddada amfaninsu a kungiyar Afrika inda yace ECOWAS a tsaye take kan kungiyar Afrika ta fannin damokaradiyya, zabe da gwamnati ta gari.

Haka nan ya kirayi gwamnatin data dage dantse kar irin hakan ta sake faruwa don zai kawo rashin zaman lafiya, rashin hadin kai da kuma rashin dawwamar kasar ta Ethiopia.

A karshe ya bayyana cewa yana yiwa kasar ta Ethiopia fatan daukaka, zaman lafiya, samun yanci da kuma cigaba.

Related stories

Leave a Reply