
Shugaban yansandan Najeriya Mohammed Adamu ya dora laifin ta’addancin Boko Haram da rogowar ayyukan laifuka a matsayin rashin tarbiyya lalalacewar tarbiyyar daga gida .
Shugaban ya bayyana hakan a wani horo da aka gudanar na kwana 2 da hadin gwiwar ragowar hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki kan yadda za’a kawo karshen ta’addanci wanda aka gudanar a Maiduguri.
Adamu ya kara da cewa idan ba’a dauki mataki da gaggawa ba za’a samu matsaloli masu nuni a cikin al’umma.
Shugaban karbar korafi daga hedikwatar yansanda ACP, Markus Ishaku ne ya wakilceshi inda yace ta’addanci fara daga rashin kula gida.

A karshe yaba iyaye shawara dasu dinga bawa yayaynsu tarbiyya ta gari.
