Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Shugaban tsaro yace za’a gudanar da hukunci ga yan kungiyar Boko Haram a watan juni

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban tsaron kasa manjo Loucky Irabor yace za’a gabatar da hukunci ga yawa-yawan yan kungiyar Boko Haram dake tsare a watan junin shekarar nan.

Irabor ya bayyana hakan ne yayin taron sauya tunani da sulhu daya wakana a Abuja.

A shekarar 2016 ne aka kaddamar da shirin Operation Safe Corridor, shiri na sauyan tunanin tubabbun Boko Haram.

Ya bayyana cewa akalla yan ta’adda dubu 1 ne aka yankewa hukunci daya kama an rufe guda dari 5 tun farawar shirin wadanda wasu zasuci shekaru daga 5 zuwa 60 a garkame.

Manjo janar Bamidele Ashafa, komandan shirin Operation Safe Corridor daya wakilce sa yace gwamnatin Najeriya ba zata lamunci ayyukan ta’addanci irin na yan kungiyar Boko Haram ba.

A baya gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, yayin taron gwamnonin Arewa da akayi a Bauchi yace kungiyar tana da bukatar sake duba ayyukan ta domin guje dama al’umma da yan ta’adda masu Hatsari
Kwamishinan birtaniyya a Najeriya, Catriona Laing ta bayyana damuwar ta a madadin gwamnatin birtaniyya game da tashin hankali da al’umma ke cigaba da fuskanta.

Leave a Reply