Shugaban Tsare – Tsare Na Majalisar Dinkin Duniya A Najeriya Yayi Alla Wadai Da Harin Konduga

Shugaban tsare – tsare na majalisar dinkin duniya a Najeriya Edward Kallon yayi alla wadai da harin da aka kai ranar lahadi a Mandarari dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya wanda yayi sanadiyyar mutum 30.

Rahoton ya fito bayan da ya fitar da sakon ga manema Labarai a Maiduguri ranar Talata.

Konduga nada nisan kilomita 38 daga gabashin Maiduguri babban birnin jihar inda ‘yan ta’addan suka kai harin kuma yana daya daga cikin wanda suka sha wahala a shekara bakwai da suka wuce.

Kallon ya kara da cewa an kai kimanin mutane 40 da suka samu raunuka asibiti a birnin Maiduguri don karbar magani.

Ya kirayi dukka bangarorin iyu dasu su dinga kare rayuwar fafren hula kamar yadda yake a dokar kare hakkin dan Adam ta duniya.

San nan ya bayyana cewa taimakon da suke bayarwa a guraren da ake fama da rikici na arewa maso gabashin najeriya na daga cikin mafi muni a duniya, Inda yace tun bayan fara rikicin a shekarar 2009 an kashe fiye da mutane 27,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *