Shugaban Kasar Najeriya Ya Bawa Kasar Guinea Bissau Taimakon Kayan Zabe

By: Babagana Bukar Wakil Ngala

Shugaban kasar najeriya Muhammadu Buhari ya amince da bada taimakon dalar Amurka 500,000, motar daukan kaya 2, akori kura 2, Babura 10, da kuma kayan aikin zabe 350 don gudanar da zabe a kasar Guinea Bissau.

Taimakon yazo bayan da suka nemi taimako daga kasashe don gudanar da zaben yan majalisu.

A rahoton da aka samu a yanar gizo na fadar shugaban kasa mai dauke da @NGRPresident, ya bayyana cewa ministan kasashen waje Geoffrey Onyema da shugaban ECOWAS Jean Claude Brou ne suka jagoranci mika kayayyakin.

Ana sa ran wan nan zai sa a samu a gudanar da zabe a Guinea Bissau cikin kwanciyar hanakali.

Haka nan ministan kasashen wajen zai leka Cotonou da Benin don mika sakon shugaba Buhari na musamman ga shugaba Patrice Talon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *