Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Ayyuka A Borno

buhari in borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Babagana Bukar Wakil

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnan jihar borno Kashim Shettima ya samar a jihar.

A kokarin farfado da tattalin arzikin jihar Borno sakamakon rikicin Boko Haram, gwaman jihar Kashim Shettima ya samar da kayayyakin more rayuwa ciki harda babban kamfani mai dauke da sassa da dama a birnin Maiduguri.

Kamfanin anyi shi ne don kera kayayyakin cikin gida kamar su ma’adanai, wutar lantarki, tsaro da dai sauransu wanda zai bude hanyar wasu kamfanonin a gaba.

A yanzu dai shugaban kasar najeriya Muhammadu Buhari ‎ya bude kamfanin da yake da sassa 16 da za’a dinga sarrafa abubuwa da dama musamman ta fannin noma ta hanyar zamani.

Ciki harda wuta mai aiki da rana da zata samar da kimanin megawatts 120 a kowace shekara. Gurin kera kujeru da tebura, abun ban ruwan rani, sarrafa tumatir, albasa, bushasshiyar citta, da abun nika kayan marmari.

Sai kuma sarrafa rogo, ruwan roba, masara, biskit, nikan gari, jakar siminti, gidan sauro, rumfar kanofi, da tabarmar leda.

Related stories

Leave a Reply