Shugaban Majalisar Wakilan Tarayyar, Yakubu Dogara Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iayyar PDP

Shugaban majalisar wakilan tarayyar Najeriya YAKUBU DOGARA ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa babbar jam’iayyar adawa ta PDP a lokacin da zaben gama gari na kasar ke karatowa.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai Magana da yawunsa Turaki Hassan, inda yace jama’a da dama daga mazabarsa wadda yake wakilta daga kananan hukumomin Bogoro, Dass, da kuma Tafawa Balewa na jihar Bauchi suka nuna farin cikinsu tare da bashi goyon bayansu sa’annan suka saya masa takardan tsayawa takara.

Mohammed Aminu Tukur, Adamu Jambil da kuma Amina Saleh sune suka jagoranci mazabaarsa da bukatarsu yayin kai masa takaddan takarar.
A cewar sa, ya amince da bukatar su na sauya sheka don tsayawa takara a zaben 2019 dake gabatowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *