
Shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan yayi alla wadai da cigaba da kashe ‘yan Najeriya a kasar Afrika ta kudu inda yace baza su cigaba da yadda da hakan ba
Lawan bayyana hakan bayan an kashe ‘yan Najeriya 118 a hare-hare daban daban cikin shekaru har da 13 da jami’an ‘yansanda suka kashe.
Rahoton ya fito daga mataimakinsa na musamman ta hanyar yada labarai da hulda da jam’a Mohammed Isa inda yace Lawan ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin jakadan kasar a Najeriya Mr. Bobby Moroe.
Moroe da tawagarsa sun kai ziyarar don bayyana wa majalisar kan binciken da sukayi kan yadda ake kashe yan Najeriya a Afrika ta kudu da kuma matakan da suka dauka na hanawa.
Shugaban ya godewa jakadan kan jawaban da kuma matakan da suka dauka da aka kashe Mrs. Chukwu.
Mr. Moroe ya bayyana rashin jin dadinsa na kisan ‘yan Najeriya a kasar tasu, san nan ya mika ta’aziyya ga wadanda abun ya ritsa da iyalansu, haka nan sun kafa kwamitin bincike kan kashe-kashen a kasar.
