Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan Ya Taya Yan Najeriya Murnan Bikin Easter .

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya taya ’yan Najeriya murna musamman ma Kiristoci da sauran Kiristocin duniya don bikin Easter a wannan karshen makon.

Lawan a cikin wata sanarwa daya fitar a Abuja ranar Alhamis, yace ya lura cewa Ista shine ɗaya daga cikin mahimman abubuwan da ke faruwa a cikin kalandar Kirista wanda shine bikin mutuwar hadaya da tashin Yesu Almasihu daga matattu.

Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan damar wajen wa’azin hakuri da addini, kauna ga makwabta da kuma jajircewa wajen sauke nauyin da ke kanmu na al’umma.

Ya ce gina babbar kasa na bukatar sadaukarwa, juriya da kumahakuri da juna. Inda yace yana da yakinin abubuwa zasu gyaru.

A karshe ya yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye ka’idojin kariya na COVID-19 tare da yin amfani da damar da za su sha maganin da aka samar kan cutar.

Leave a Reply