
By: Babagana Bukar Wakil Ngala
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya sauka daga mulkin kasar, rahoton da gwamnatin kasar ta fitar ya bayyana cewa ana nan ana duba yadda za’a kula da kasar inji ministan kasar.
Ministan ma’adanai dake arewacin Darfur, Adel Hussein, ya bayyanawa gidan talabijin nna Al-Hadath dake Dubai cewa ana tattaunawa kan yadda za’a ba sojoji rikon kasar bayan saukar shugaba Al-Bashir.
Rahoto ya fito daga Sudan cewa al-Bashir na gidan gwamnatin kasar cikin tsaro, an kuma baza jami’an soja zuwa Khartoum.
Haka nan an baza jami’an tsaro ma’aikatar tsaron kasar, kan manyan tituna, manyan gadoji a fadin Khartoum kusa da inda Al-Bashir din yake.
Tun 19 ga watan Disamba Sudan din take cikin rikici da zanga-zanga tunda gwamnatin tace zata kara kudin Biredi, da rikicin tattalin arziki da ya janyo karancin mai da kudade.
Bashir ya karbi shugabancin kasar tun 1989, wanda hakan yasa turawa suke so su karya shi.
Kotun laifuffuka ta duniya ta zargi Bashir da kisan kiyashi over allegations of genocide in Sudan’s Darfur region during an insurgency that began in 2003.
Fada ya barke ranar Talata tsakanin sojoji da yan zanga-zanga inda mutuum goma 11 suka rasa rayukan su ciki harda jami’an tsaron kasar.
