
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi buda baki da gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da sarkin Maradun, Garba Tambari ranar lahadi a kasar makka.
Mataimakin shugaban kasar na musamman ta fannin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Lahadi.
Yayin shan ruwa shugaban ya bayyana rashin dadin dadin yadda ake rasa rayuka da dukiyoyi a jihar Zamfara sakamakon hare-haren da suke fama dasu na yan bindiga.
Sarkin Maradun ya jagoranci addu’ar da akayi yiwa wadanda harin ya ritsa dasu a jihar Zamfara da kasar najeriya gaba daya.
Shehu ya kara da cewa shugaban ya samu rakiyar shugaban ofishin jakadancin Najeriya a kasar Saudiya Justice Isa Dodo da kuma ma’aikatansa.
