
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan harin da yan bindiga suka kai kauyuka 3 dake karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto State dake arewa maso yammacin Najeriya inda aka kashe mutane da dama.
Rahoton ya fito daga bakin mai Magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu, inda yace shugaban yayi addu’at samun sauki ga wadanda suka samu raunuka.
Haka nan yansandan yankin sun kama wasu daga ciki, san nan shugaban yayiwa wa gwamnan jihar Aminu Tambuwal gaisuwa na wadanda suka rasa rayukansu.
Shugaban yayi alla wadai da irin wadan nan hare-hare da ake kaiwa al’umma da basu jiba basu gai ba.
Ya tabbatar wa ‘yan najeriya cewa gwamnatinsa baza ta gaji ba wajen yaki da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da kuma mmasu garkuwa da mutane.
