
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin kunar bakin wake da aka kai a wajen kalloa kauyen Mandarari dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya.
Cikin sakon ta’aziyyar shugaban ya koka da harin inda ya jaddada cewa duk wanda suka kai harin su jira sakamakonsu daga shari’a da kuma gurin Allah.
Haka nan ya kirayi jami’an tsaro dasu dage dantse wajen ganin ‘yan ta’addan basu kara samun nasara ba.
San nan yayi addu’a kan Allah ya jikan wadanda suka rasu yabawa iyalansu hakuri.
