
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci babban mai shari’a na kasar najeriya kuma Ministan shari’a Barr. Abubakar Malami da yayi gaggawar shiga Tsakani kan shari’ar wata daliba yar najeriya mai suna Zainab Aliyu da hukumomin Saudiyya suka samu da kwayoyin da aka saka mata.
Mai bawa shugaban kasa shawar ta musamman Abike Dabiri-Erewa ce ta fitar da rahoton a Abuja ta hannun mataimakinta ta bangaren yada labarai Abdur-Rahman Balogun a Abuja inda yace shugaban ya bada umarnin tun sati biyu da suka wuce.
Zainab wacca ta gama karatunta a jami’ar Maitama Sule University dake Kano, an tsare ta bayan an samu bagananin tramol a Jakarta wanda ke dauke da lambar fasfo dinta, inda wasu suka saka mata.
Dalibar sun tashi daga filin tashin jirage na Malam Aminu Kano International Airport da mahaifiyarta Hajiya Maryam Aliyu, da yar uwarta Hajara Aliyu amma aka kamata sakamakon jakar mai dauke da sunanta, inda aka kamata a inda suka sauka a kasar.
