Shugaban Kasar Najeriya Ya Samar Da Jirage Guda 2 Na Yaki

AIR
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya samar da jiragen helicopter guda 2 na yaki ga rundunar sojojin saman Najeriya.

Rundunar ta fito da jiragen guda biyu yayin murnar cikarsu shekaru 55, shugaba Buharin bai samu halarta ba inda yake hutu na kwana 10 a kasar ingila, mataimakinshi Yemi Osinbajo ne ya wakilce shi.

Ya bayyana cewa yana daya daga cikin ayyukan gwamnati kan ta samar da kayyayakin don a kawo karshen ta’addanci da kare yan kasa.

Haka nan ya bayyana jin dadinsa na yadda aka baje kolin kayan da yadda jami’an suka suna nuna bajintarsu daga mazan har matansu yayin fareti.

Shugaban ya yabawa shugaban rundunar Air Marshal Sadique Abubakar da ma’aikatansa kan yadda suke tafiyar da rundunar.

Buhari ya kara yabawa jami’an kan yadda suke yaki da yan kungiyar Boko Haram

Related stories

Leave a Reply