Shugaban Kasar Najeriya Ya Kirayi Jami’oi Da Su Dinga Kirkirar Sababbin Abubuwa

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhar ya kirayi jami’oin dasu dage wajen kirkiro sababbin abubuwan da zasu kawo cigaban kasa.

Buhari yayi wan nan kiran a jami’ar Dutsinma dake jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya yayin bikin yaye dalibai karo na 4.

Shugaban, wanda tsohon gwamnan Kano farfesa Hafiz Abubakar ya wakilta ya bayyana cewa wan nan kiran anyi shi ne don ya zaburar da jami’oin kasar ne
Binkice, zurfaffan tunani, binciken sababbin abubuwa ya kamata jami’oin su bada karfi akai kamar yadda ake a ragowar jami’oin duniya.

Haka nan ya kalubalanci jami’oin wajen yin sanyi ta fannin binciken sababbin abubuwa da kirkirarsu, inda yace acikin shekara 58 na samun yancin kai har yau sun abaya.

San nan ya bayyana cewa gwamnatinsa zata cigaba da kokari wajen yin duk abinda ya dace don bunkasa jami’oin ta hanyar hukumar TETFUND.

Buharin ya kirayi jami’ar da ta hada kai da hukumar Sokoto River Basin Development Authority su samar da kayan amfanin gona na zamani cikin fasaha ga manoman yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *