Shugaban Kasar Najeriya Ya Halarci Taron Zuba Jari A Kasar Dubai

buhari dubai
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya isa kasar Dubai ranar Lahadi.

An samu rahoton daga shafin jam’iyyar APC dake Twitter na kafar sadarwa inda suka wallafa cewa, shugaban yaje kasar Dubai din ne don ya amsa gayyatar da mataimakin shugaban kasar Sheikh Mohammed Bin Rachid Al Maktoum yayi masa.

Shugaban ya je kasar ta dubai ne don ya halarci taron da suke gudanarwa duk shekara na saka jari wanda wan nan shine karo na tara (9).

An bayyana cewa shugaba Buharin na daga cikin manyan baki, inda zai gudanar da jawabi kan wasu bayanai.

Taron zai budewa kasashe kimanin 140 hanyar samun masu neman zuba jari da kuma hada su da yan kasuwa da suke da niyyar shiga kasuwanci.

Related stories

Leave a Reply