Shugaban Kasar Najeriya Ya Bayyana Alhinin Rasuwar Umar Tudunwada

Tudunwada3
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa na rasuwa mataimakin shugaban Nigerian Guild of Editors Malam Umar Sai’du Tudun-Wada.
Tudun-Wada, shine Manajan Darakta na hukumar Radiyon Kano, ya rasu ranar Lahadi a hatsarin mota da ya ritsa dashi daga Abuja zuwa Kano.
A rahoton da mataimakin shugaban kasa na musamman ta fanni yada labarai da hulda da jama’a Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja ranar Lahadi ya bayyana cewa Buhari ya bayyana tsohon dan jaridar a matsayin mutuum na gari wanda ya rike aikinsa da kima da daraja.

Ya kara da cewa yana alfahari da marigayi Tudun-Wada wanda yayi iyakar kokarinsa kan aikinsa.

Ya mika sakon ta’aziyya ga Guild of Editors, gwamnatin Kano da kuma iyalan Tudun-Wada. Allah ya basu hakurin jure rashinsa ya kuma saka mishi aljanna.
Gidan Radiyon Dandal Kura International sun rawaito cewa Tudun Wada ya samu mummunan hatsarin mota yayin da yake dawowa daga Abuja da daya daga cikin matansa da ‘yarsa.

Marigayi TudunwadaHe yayi sakataren kungiyar yan jaridu a kano daga 1990 to 1992, yayi Executive Director a gidan radiyon Dandal Kura Radio International dake Maiduguri daga 2015 zuwa 2017 a yanzu shine mataimakin shugaban NGE.

Tudun Wada ya kai kimanin fiye da shekara 35 yana aikin jarida a Najeriya. Anyi jana’izar sa a gidan sa dake kan titin Zoo Road dake kano kamar yadda addinin mususlinci ya tanadar, tuni dai aka binne shi a makabartar Tarauni.

Related stories

Leave a Reply