Shugaban Kasar Najeriya Ya Bada Umarnin A Sulhunta Masu Rikici A Adamawa Da Taraba

Shugaban kasar najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarni da gaggauta sasansa tsakanin masu rikice-rikice a jihohin Adamawa da Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya.

Air Commodore Akube Iyawu daraktan bincike da ceto jama’a a hukumar bada agajin gaggawa na kasa wato NEMA ne zai jagorancin sulhun inda tuni ya isa Yola babban birnin na jihar Adamawa.

Akube ya bayyana cewa ya ziyarci guraren Hamman Bata da Haman Bachama dake Demsa da Numan, inda yace sunje ne su ganewa idonsu irin barnar da akayi musu bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci da suje su ganewa tidonsu barnar da akayi kuma su sulhunta tsakaninsu.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya zata sulhunta ta hanyar NEMA cikin karamin lokaci.

Mr Stephen Irmiya da ya fito daga Hama Bachama da wani Alhamdu Teneke dake Bata sun godewa shugaban kasar da ya tuna dasu a halin da suke ciki.n Haka nan sun bukaci gwamnati da samu hanyoyin kawo karshen rikicin don a samu a zauna lafiya.

Dr. Muhammed Sulaiman babban sakatare na hukumar a jihar Adamawa ya bayyana cewa yan ta’adda sun kai hari kauyen Bolon da Barai inda aka kashe mutuum biyu, mutuum 10 suka samu raunuka inda aka kona gidaje da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *