Shugaban kasa Buhari Ya Mika Sakon Bikin Kirsimeti Ga Yan Najeriya

buhari speech 22
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya dukkan yan najeriya murnar bikin kirsimetin wannan shekakara ta 2020.

Shugaba Buhari yace bikin kirsimetin yana gabatar da murna, zaman lafiya, da fata nagari tare da cewa ana tsananin bukatar irin kyawawan dabi’u da Al-masihu ya nuna a najeriya musamman ma a wannan lokaci da ake fama da matsalolin yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da karyewar tattalin arziki dama karuwar annobar COVID-19.

Shugaba Buharin ya nemi jama’a dasu rungumi fatan alheri dake tattare da bikin na kirsimeti kuma su sake yadda da muradin gwamnati na adana zaman lafiya tsaro da ci gaban najeriya.

Leave a Reply