Shugaban Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ,ya Bukaci Da A Gaggauta Dakatar Da Tawagar ‘Yan Sandan Ta Musamman.

Shugaban hukumar ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya bukaci da a gaggauta tarwatsa tawagar ‘yan sandan Special Tactical Squad.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Jimoh Moshood, shima ya bu’kaci da a sauya mambobin tawagar zuwa wani sashe.
Ya ce wasu daga cikin manyan tawagar da suka shiga gidan Cif Edwin Clark ranar 4 ga watan Satumban wannan shekarar a unguwar Asokoro dake birnin Abuja ba tare da izini ba ana gudanar da bincike a kansu.
Moshood ya kuma nemi da a gaggauta tarwatsa tawagar ba tare da 6ata lokaci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *