Shugaban Buhari Yayi Bikin Ranar Yara

shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bikin ranar yara inda yayi alkawarin barin kasa cikin inganci ga yara na yanzu da masu tasowa.

Domin murnar bikin na ranar yara da ake yi kowace ranar 27 ga watan Mayu, shugaba Buhari ya karbi bakwancin tawagar yara a fadar shugaban kasa.

Hakan ya fito ne ta hannun mai taimakawa shugaban na musamman kan harkokin aa labarai Mal. Garba Shehu.

Yayin taron an yanka cake tare da zazzaga ofishin shugaban kasa, dakin taro, dakin cin abinci da kuma wajen ajiye dabbobi.

Daga karshe yace yara rahama ne, wanda za’a tarbiyatar domin daukar nauyin al’umma a gaba.