Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Shugaba muhammadu Buhari Yace Gwamnatinsa Zatayi Amfani Da Dumbin Albakatun Iskar Gas A Kasar

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba muhammadu Buhari yace gwamnatinsa zatayi amfani da dumbin albakatun iskar gas a kasar don bunkasa tattalin arziki dakuma bunkasa masana’antu.

Shugaban ya bayyana hakan ne a taron share fage na taron koli na kungiyar man fetur ta kasa da kasa a shekarar 2021 dakuma kaddamar da shekarun gas na gas a abuja.

Shugaba Buhari yace idan akayi la’akari da irin karfin da kasar ke da shi na kimanin cubic feet na gas tiriliyan 600, kayan na da karfin gaske wajen fadada tattalin arzikin kasar.

Yace sanannen abune cewa najeriya kasa ce ta gas wacce take da dan karamin man fetur, amma kasar tafi maida hankali kan mai a shekarun da suka gabata.

Wannan shine sababin da wannan gwamnatin ta yanke shawarar tunkara lokacin da muka ayyana shekarar 2020 a matsayin shekarar gas a najeriya.

Kafin ayyana shekarar 2020 a matsayin shekarar gas, wannan gwamnatin ta nuna jajircewa ga cigaban arzikin albarkatun iskar gas na najeriya da kuma karfafa jerin iskar gas ta hanyar yin bita da fitar manufofi da ka’idoji don bunkasa ayyuka a bangaren kamar yadda aka killace a kasar manufofin gas na shekara ta 2017.

Leave a Reply